(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Iran ta musanta zargin kasar Amurka da wasu kafafen yada labarai kan cewa jami’an tsaron kan iyakar kasar ne suka azabtar da wasu ‘yan gudun hijiran Afganistan 57 sannan suka jefa su cikin kogin Herat a kasar ta Afghanistan.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif yana mayarwa Alice Wells mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurka ta wucin gadi a kan harkokin kudancin Asia da martani, kan lamarin.
Kafin haka dai Jaridar Khaama Press News Agency ta turanci ta kasar Afganistan ta buga labarin wanda yake cewa mutane 23 daga cikin 57 da aka jefa a cikin kogin Herat na kasar ta Afganistan sun mutu. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Afgnasitan ta ce ta fara bincike kan lamarin.
Gwamnatin kasar Iran dai, ta yi allawadai da kisan, sannan ta kara da cewa an aiwatar da kisan ne a bangaren kasar ta Afganistan da ke lardin Herat na kasar ta Afganistan.
A halin yanzu dai yan kasar Afganistan kimanin miliyan 3 ne suke rayuwa a kasar Iran, Sannan fiye da miliyan 2.5 daga cikinsu ‘yan gudun hijira ne daga kasar ta Afgansitan tun fiye da shekaru 40 da suka gabata.
Zarifa ya ce kasar Amurka wadde ta mamaye kasar Afganistan kimanin shekaru 20 da suka gabata ita ce da alhakin tilastawa mutanen kasar barin kasarsu.
/129
7 Mayu 2020 - 04:38
News ID: 1034347

Gwamnatin kasar Iran ta musanta zargin kasar Amurka da wasu kafafen yada labarai kan cewa jami’an tsaron kan iyakar kasar ne suka azabtar da wasu ‘yan gudun hijiran Afganistan 57 sannan suka jefa su cikin kogin Herat a kasar ta Afghanistan.